|
Furodusoshi mata, ku hada kanku don tsira da mutunci
Daga Danjuma Katsina
Hajiya Nana Lili Katsina
|
IDAN ana maganar wasan kwakwayo a Katsina, to tilas ne a ambaci Hajiya Nana Lili, daya daga cikin shahararrun 'yan wasan fim na Hausa. Nana Lili fitacciyar 'yar jarida ce wadda ta rike mukamai a kungiyoyin aikin da kuma na mata a lokuta daban-daban, kuma kwararriyar ma'aikaciyar aikin rediyo ce. Ta yi fice a wasan kwaikwayo na talbjin din Katsina, wato Ramin Kura, kuma ta fito a finafinai kamar Kogin Bagaja, Kowa Ya Yi Da Kyau, Alaqa, da sauransu da dama.
Mun dade da yin wannan hirar da Nana Lili, tun kafin a kafa Kungiyar Furodusoshi Mata ta Jihar Kano (WEPA). A hirar, Nana ta kawo shawarar a kafa kungiya irin wannan wadda za ta kare hakkin mata a sana'ar fim. To, duk da yake yanzu akwai kungiyar, iyakarta Kano kawai, kuma ko can din ma akwai matsaloli na rashin hadin kai, wadanda Nana ta yi tsokaci kan irinsu. DANJUMA KATSINA ne ya tattauna da wannan 'yar wasan 'yar shekara 36 a birnin Dikko. A sha labari daga bakinta:
Fim: Malama, za mu so mu ji tarihinki da farko.
NANA: Assalamu alaikum. Da farko dai ni haifaffiyar Katsina ce kuma an haife ni a unguwar Sararin Kuka, ta Karamar Hukumar Katsina cikin Jihar Katsina, a cikin 1966. Na yi makarantata a nan 'Sararin Kuka Primary School' da ken nan cikin garin Katsina. Bayan nan a shekarar 1978, na tafi Kwalejin Sarauniya Amina da ke Kaduna, daga shekarar 1983 na samu canjin makaranta na dawo makarantar 'yan mata da ke Kankiya, na gama makaranta a 1983. Aka yi mani aure a shekarar 1984. A 1985 Allah ya albarkace ni da haihuwar da namiji, wanda a halin yanzu ya rasu.
To daga nan a 1988 sai na fara aiki da kamfanin kafet na Katsina, wato 'Hamada Carpets.' Daga nan na yi 'yan watanni uku na dawo MAMSER. To bayan nan sai na koma Ma'aikatar Labarai ta Jihar Katsina a 1989. Daga nan sai na rika samun canje-canjen aiki, inda na yi iki a gidan Rediyon Jihar Katsina wacce take hade da gidan talbijin na jiha, wato KRTV, har shekara bakwai. To bayan nan ne kuma ina nan sai na samu admission ina na je na karanta aikin jarida a Abuja. Daga nan na samu canjin aiki na koma Karamar Hukumar Katsina a 2001. A yanzu ina da da guda daya wanda ake kira Saifullahi.
A wace shekara kika faa fitowa a wasan kwaikwayo, kuma da wane wasa kika fara?
NANA: E to, wasan kwaikwayo na fara a lokacin ina sakandare kuma ni ce sakatariyar kungiyar wasan kwaikwayon. Sa'annan na fara wasan kwaikwayo a cikin Jihar Katsina a gidan talbijin na Jihar Katsina. Amma kafin nan, fim din da na fara yi, wanda a lokacin ba a saba da finafinai ba, shi ne fim din Drug Abuse (a kan illar shan miyagun kwayoyi). Amma ina wasan kwaikwayo a gidan rediyo na Jihar Katsina, a cikin kungiyar Ramin Kura.
Daga lokacin da aka fara finafinan kaset, wane wasa kika fara fitowa?
NANA: Fim din da na fara na farko shi ne Kogin Bagaja wanda na yi sina-sinai guda biyu, na fito a 'yar sarki. Daga nan sai na yi fim din 'Mandawari Enterprises' da Executive Producer din, Alhaji Habibu Sani Kofar Soro, wanda har yanzu fim din bai fito ba. Bayan shi kuma na yi fim din Alaqa, na yi fim din Kowa Ya Yi Da Kyau. Wasu ma ba zan iya tuna su ba tunda yanzu an dau lokaci.
Yanzu akwai wata kungiyar mata da kike ciki. Wane matsayi kike rike da shi a cikinta?
NANA: E to na shiga kungiyar nan ta mata mai suna NCWS, sai dai memba ce ni a ciki. Na taba rike sakatariyar kudi ta kungiyar 'yan jarida ta Jihar Katsina ta kasa wato NUJ. To amma a halin yanzu na dan sauka.
A cikin 'yan wasan fim waye ya fi burge ki kuma me ya sa yake burge ki?
NANA: A gaskiyarsa in aka ce dan wasa, a ganina shi ne wanda zai fito ya yi wasa kamar da gaske, kuma ya isar da sakon da ake son ya isar kuma ya gamsar da 'yan kallo, shi ne zan iya ce ma gwarzona. Saboda a yanzu in aka ce mutum ya shekara talatin ko ma arba'in, ko kuma in ce ma tunda aka fara wasan Hausa yake fitowa, to idan dai ya kasa isar da sakon ko ya kasa gamsar da 'yan kallon to ni wannan ban ma dauke shi dan wasa ba, na dauke shi mai bata fim da kuma bata al'adun Hausa.
Wato ke kina nufin duk wanda zai gwada hikimar da Allah ya yi masa ta gamsar da 'yan kallo shi shi ne gwarzonki a lokacin da yake yi.
NANA: Kwarai da gaske. Don irin wadannan a lokacin in suna yi a matsayina na 'yar wasa sai in ji tsigar jikina na tashi, sai in ji kamar in shiga in yi masa kyauta wacce take ta musamman ce, ta nuna cewa ni ya burge ni kuma ya gamsar da ni.
Kuma kina nufin komin kwarewar dan wasa in har ya kasa gamsar da dan kallo yakan fitar maki daga rai?
NANA: Wannan ma ba dan fim ba ne ko dan wasa, bata-gayya ne da kuma bata al'adun Hausa. Kuma ba zai fito gabana ya ce min wai shi dan wasa ba ne ko kuma gwani, kawai dai zan kalle shi a matsayin ya yi shiri. Ka san su kansu masu kallo akwai sakon da ko wani abu da idan mutum ya yi yakan burge su, ka ga idan za a ce mutum a sa ya yi kuka kuma a ga kukan sosai, ko kuma a ga alamar cewa fuskar shi yana cikin abin damuwa, ka ga wannan ya nuna abu ne kamar da gaske aka yi. Ka ga irin wadannan suna burge ni kwarai da gaske. Amma don ka yi fim ka ce ai tun kan a haifi wane nake yi amma ka kasa yi, to ai ni ban dauke ka ka iya komai ba.
Ka ga misali kamar yadda ake shirya finafinai, wato idan ina so in gwada maka wanda ya fi burge ni a duka, kila kakan so ka ji wane yake burge ni. To wanda ke burge ni bayan darakta yake, wato a matsayina na ina yin finafinai kuma ina yin wasan kwaikwayo na Hausa da kuma yanayin karatun da na koyo a bangaren jarida. Shi darakta shi ne kashin baya na fim kwata-kwata. Meye kashin baya? Ka ga akwai wasu gurare wadanda za ka ga mutum ya kasa amma sai ka ga darakta ya yi kokarin yadda zai sa ya yi. Kamar yanzu a ce yi kuka, sai mutum ya yi bai iya ba, ka san wani da wuya ya yi kuka. Sai darakta ya ba ka lokaci. Wani daraktan ma sai ya bari zai so sai ranka yana baci, sai ya ce sannan yake son a yi abin. Ka ga kenan lokacin zai samu abin da yake so. Wani in ranka baci yake sai ya bari kana cikin annashuwa, in annashuwa yake son kai mai sai in ya ga kai mai. Yanzu ka dauki misali a wasu lokuta za ka ga kamar an hada sin kamar mutum biyu, za su hadu a fim daya su yi magana sai daya bai nan, sai darakta ya dauki wannan; kila wancan din yana da wasu 'yan harkokinsa da zai yi sai ya ce ya je, idan ya tafi idan wancan ya zo za ka ga ya dauki wannan. Kai a matsayinka na kana zaune kana kallon lokacin shiryawar sai ka ce ya za a dauki wannan a dauki wannan? To sai ka ga wannan na magana wannan na ba shi amsa. Kuma a inda wancan din ya yi a nan za ka ga an zaunar da wannan din. Za ka ga guri daya suke zaune ba bambanci. To ka ga irin wannan ba karamar fasaha ba ce, ba kuma karamar baiwa ba ce Allah ya yi ma daraktoci. Yanzu misali ka daukar min kamar darakta Tijjani Ibraheem yana bakin kokarinsa, sannan wajen Hafizu Bello, ka je wajen Ishaq Sidi Ishaq, shi ma ba daga baya ba, Zilkifilu Muhammad shi ma ba daga baya ba, balle a zo wajen su Bala Mohammed Makosa, a dawo wajen su Ado Ahmad Gidan Dabino, wato wadannan mutanen suna bakin yin su, kuma a gaskiya idan ana ba da dubu bisa dubu ba dari bisa dari ba, ni ina iya ba su. Kuma akwai sauran wasu daraktocin wadanda wadansu ban san sunansu ba, amma suna bakin kokarinsu. Gaskiya in aka ce maka darakta to ni darakta yana burge ni kwarai da gaske.
Kwanan nan an fara samun mata furodusoshi. Me za ki ce a kan wannan?
NANA: Ina da abubuwan cewa saboda an ce ciwon mace na mace ne. Kamar yadda Hajiya Balaraba Ramat, Hajiya Zayya Dantata, Hindatu Bashir, Maryam Mashahama da su Rabi Sulaiman da Amina Lamido suka fito a matsayin furodusa suka sadaukar da kansu da dukiyarsu, sukai kokari suka shirya finafinai, a gaskiya sun burge ni kwarai da gaske. To amma abin da nake so gare su ko nake kira gare su alfarma ce nake nemar wa 'yan'uwanmu mata. Meye alfarma? Idan sun shirya fim su rika jawo matan nan jikinsu, suna sa su cikin finafinansu. Saboda akasari akan ce furodusoshi ba su sa mace a fim din su sai sun biya bukatarsu da su. To ai mace ba wata bukata da za ta biya ga mace 'yar'uwarta. In aka ce mata furodusoshi suna jawo mata suna sa su a fim din su, za ka ga abin ya zama kalubale tsakanin mata furodusa da maza furodusa, ka ga kenan ya kamata su wadannan mata furodusa din ya kamata su zauna su hada kansu. Idan suka taru suka hada kansu zai zama irin abin nan ne da ake cewa what a man can do a woman can do better, wato abin da namiji zai iya yi mace ma za ta iya yin shi. Haka kuma yawancin furodusoshi na waje ko kuma in ce wasu 'yan wasa mata na waje da na cikin gida kamata ya yi idan matan nan sun jawo ku jiki ku yi musu abu, kar ki nuna cewa wai ni don ina daura oganza wai ke kina daura wacce wace, mu dauka duk daya ne. Kuma wanda ya kirawo ka ya sa ka cikin sana'arshi, ai da suka kirawo mu, sun sa mu ne domin mu samu arziki. To bai kamata ka wulakanta mutum ba. Haka kuma mu matan nan wadanda ke yin shirin finafinai ko kuma wadanda suke fitowa a finafinai kamata ya yi mu zama masu kama, ya zamanto cewa mun tserar da mutuncinmu, ya kuma kasance mun bai wa 'yan'uwan nan namu mata goyon baya dari bisa dari. Saboda nan gaba da an tashi in wani darakta zai yi fim in ya ce ai wacce zai sa sai ki ce a'a ni ma ina da wace nake so. To a ta haka za mu rinka jawo mata 'yan'uwa jikinmu, ya zamana suna kaunarmu. Za ka ga inda wata ta fito a wani fim ta ga za a cuce ka ta ga za ta iya taimaka maka sai ta ce a'a saboda ka taba fitowa a fim din ta kuma a taimaka mata.
Wadanda suka gwada cewar su suka iya komai kuma suke ganin cewa mace sai ta zo ta yi wata bajinta, ko kuma ka yi ana cewa ai wannan ba ta da kaza, ba ta da kaza. To idan mace ce 'yar'uwarka to baruwanta da wannan. Ita kawai abin da za ta yi kawai ta dauko ta saka. Haka kuma ga kamar furodusa mata na waje ya kamata idan suna so su san wacece ta iya wacece ba ta iya ba a cikin akta, suna su iya su yi wani dan kokari haka su tsamo can gari, su tsamo can garin a samu cikin guruf-guruf na garuruwa haka, sai su tsamo sai su gwada, su samu wani fim su gwada su gani, shin yaya abin yake? Ba kullum mutum zai tsaya a fuska daya ba, don tsayawa a fuska daya wani lokaci yana kashe mutum. Ran da duk aka ga ba wane ba za a yi ba. Saboda yawanci in dai ba a ga bullowar wadannan matasan ba wani cewa ya yi daga yin auren Fati ya gama kallon fim . To amma in ana ta yamutsawa ana ta hadawa, sai ka ga idan mutum ya ga fim din wannan ya ga na wannan da ya ga hoton waccan a kwali sai ya ce kai ai ita ma lafiya lau ne zai saya. Saboda haka nake kira ga sauran 'yan'uwanmu furodusa mata da su hada kansu gaba daya. Don Allah kar su bari wani ya shiga tsakaninsu kuma kar su bari a ji kunya, tunda an ce sai bango ya tsage kadangare ke samun wajen shiga. Wato abin da nake nufi, idan sukai kungiya suka zabi wasu shugabanni wadanda suke masu rikon amana ne da sauransu, to za ka ga cewa su ma kungiyar nan na furodusa maza ko da yake hade take. Ka ga abin nufi a nan shi ne, wato kamar yadda ake samun kungiyoyin maza a samu na mata, ka ga kamar 'Arewa Film Producers'. Ka gani idan su wadannan furodusa mata za su iya su ma in suka hada su ma tasu kungiyar suna iya zama ta mata ce daban, amma kuma suna dan samun shawarwari gurin mazan. Saboda ai za su iya, meye za su iya? Ai dai mata iyaye ne, kuma duk abin da namiji ya kamanta, haka kuma mace ma za ta iya kamantawa ta yi, kuma idan kuma a cikinsu akwai mata wadanda suke yi fice, misali a sararin duniya, ka ga akwai Balaraba Ramat ta yi fice wajen rubutu tun ana ma kungiyar marubuta ta littattafai. Ka ga akwai wasu kuma irin su Hindatu da sauransu. To idan akai haka ka gani za su ji dadi, za su kuma taimaka wa kansu. Yanzu misali in ka dauki a bangarenmu na jarida akwai kungiyar 'yan jarida ta kasa, wato NUJ, mu muna cikinsu maza, sai muka rika ganin wasu abubuwan mu muna son mu yi amma kuma mazan sun fi mu yawa sai muka zo sai muka shawarta muka yi kungiyar mata, wato NAWOJ. Ka ga duk mu mata ne mu je mu kintsa mu yi rikita-rikita mu je mu duba. Sannan kungiya ta kasa ga baki daya, wato NUJ, sai mu zo sai mu nemi shawara mu gyara. Ka ga irin haka idan suka fito su ma za su samu ci gaba ba dan kadan ba.
Yanzu ana ganin mu Arewa kullum matanmu kanmu kamar ja baya muke. To kamata ya yi mu ma mu shiga cikinsu yadda za a ga cewa idan gabacin Nijeriya ko yammacin, ko kudancin sun yi, to a ga matan Arewa ma yau sun fito suna yi. Saboda muna ganin abubuwa da dama ma furodusas mata ina ba su shawara su hada kansu su yi wannan kungiya ta mata su samu shuwagabanni wadanda kungiyar nan za ta yi karfi har ma in ce ta kai iyakar yadda za a ce an kasa yadda za a kai an fasa kungiyar, ka ga kamar abin da ya sa ka ga ina ta wannan babatu na cewa su hada kai, su zaman tsintsiya madaurinki daya. Saboda wani abin wanda ni a nawa ganin suna burge ni, wato abin da ya sa na ce maka suna burge ni wani lokaci yadda suka hada kansu ka ga kamar yadda suke maida himma kwarai da gaske abin yana burge ni saboda ni ma a yanzu haka a rayuwata, ina so in ga na zama daya daga cikin furodusas ba wai don wani abu ba, don kawai in ga na daukaka al'adunmu na gargajiya, na daukaka harshen Hausa. To ina matukar kaunar in gan ni a cikinsu wanda na san ta haka ni ma zan taimaka ma 'yan'uwana kuma su ma za mu samu hadin kai har mu samu fahimta da su tunda ni ma zan shiga ba wai ina nufin wai ko ina nufin wai ta bangaren wani samun kudi ba ko wani abu, a'a. Ni dai kawai ta bangaren in ga na taimaka ma harshena na Hausa. In sa kudina in ga na fito a matsayin ni ma furodusa ce, in shiga cikin furodusas din saboda mu dada samun kwarin gwiwa kuma mu kara fito da wasu matan wadanda yanzu suke shiga cikin harkar fim.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|