MASU karatunmu sun sha aiko da wasiku don jin tarihin wanin fataccen dan rawa wanda kuma yawanci ba su san sanansa ba, sai sukan rika kiransa da suna "mai sankon nan". Hakika saboda gwanancewar da ya yi ne wajen iya taka rawa, juyawa, da kuma karya gabobin jikinsa ne yake burge mutane. A wannan wata an samu tattaunawa da shi wannan gwanin rawa mai suna Ali Tarauni wanda aka fi sani da suna Lilo. Koda ya ke dai shi ya ce "rawa ba ta da gwani".
A wajen rawa dai Lilo ya yi masu zarra. Na farko dai ga kwarewa, ga shi kuma dalilin rawa ya je kasashen da mafi yawan 'yan fim sai dai su ji labarinsu. Wadanne kasashe ne ya je? Shi da su wa suka tafi? Wane dan wasa ne ya fi jin dadin rawa a bayansa? Shin sankonsa na halitta ne? Duk a cikin wannan hira za ku ji amsoshin wadannan tambayoyin da kuma labarin targade, gocewa da gurdewar da ya taba yi a dalilin rawa.
Lilo, wanda kuma dan wasa ne, mutum ne mai yawan barkwanci da nishadi. Wannan ya kara masa farin jini da masoya a tsakanin jama'a. Ali Tarauni, wanda ma'akaci ne a Hukumar Tarihi da Inganta Al'adu ta Jihar Kano, ya ce ba shi kadai ba ne dan rawa. "Rawa gado ce, al'ada ce; idan ba ka yi ba, to ubanka ya yi. Idan bai yi ba, kakanka ya yi." Haba Lilo, me ya yi zafi haka? Ku karanta ku ji dalili.
FIM: Lilo ina ne asalinka?
LILO: To asalina ni Bahaushe ne kuma mutumin Kano. An haife ni a (unguwar) Tarauni, haka kuma na yi karatu a makarantar firamare ta Tarauni A takaice shekaruna talatin daidai. Bayan na kare makarantar firamare, na yi karatu a JSS Sabuwar Kofa, daganan na tafi GSS Gwammaja inda na gama sakandare. Bayan na kare na yi karatun difiloma a sashen 'Public Administration' a FCE, ta Kano.
Kafin harkar fim mutane sun ga wani dan rawa dogo maras jiki yana rawa a talbijin tare da Funmi Adams wacce ta yi wakar "Ina Gizon Yake?" An ce wai kai ne. Shin kai din ne kuwa?
LILO: Don ni din ni ne. Ita Funmi Adams ita kadai ta zo. Daga ofishinmu na Hukumar Tarihi da Inganta Al'adu, aka bai wa wannan shiri nata tallafi.
A wace shekara?
LILO: Ba zan iya rikewa ba, gaskiya na manta.
Shekararka nawa kana aiki a Hukumar Tarihi da Al'adu?
LILO: Yanzu na shekara ta kai 14 tare da ita.
To kana ba mu labarin Funmi Adams. Ci gaba.
LILO: Lokacin da ta zo daga Legas ta gana da daraktanmu, shi kuma ya tura shugaban fannin wasanni, aka zauna aka shirya abin da ta yi.
Wato wakar "Ina Gizon Yake?" a Kano aka yi ta kenan?
LILO: E, a nan ne. An je Gwarzo an yi, da kuma sauran wurare.
Ban da wakarta ka taba fitowa a matsayin dan rawar wani mawaki ko da ba Bahaushe ba ne?
LILO: Kamar wanda bai shafi fim din Hausa ba haka da sauransu?
E..
LILO: Kwarai kuwa. Akwai wadansu raye-raye da wake-wake da muka yi tare da wani mawaki mai suna Alex Zito wanda ya zo nan shi ma Kano. Akwai kuma wasu da yawa da kan zo daga cikin wasu kasashe na Afrika. Idan sun zo da wakarsu mu kuma sai mu shirya raye-raye da za a hada da wannnan waka tasa don ya samu yadda yake so.
A wace shekara ka fara yin rawa a finafinan Hausa? Kuma a wane fim ka fara?
LILO: E, to rawa dai a takaice a fim din Hausa ma gaba daya akwai wani fim kwaya daya wanda shi ne aka fara yin rawa a fim din nan Kano a cikinsa. Wannan fim shi ne Wake Daya. Daga shi sai Sa'a Ta Fi Gata. Sai kuma sauran finafinai.
Da Wake Daya ka fara waka kenan?
LILO: Ba ma ni ba, kowa ma, wanda ya fara rawa ina ji mu uku ne a maza-da ni Ali Tarauni da Lilisco da kuma Muntari Kwanzuma. Mu ne muka fara yin rawa a maza sai kuma wadansu 'yanmata da muka diba.
A ina ka samo sunan Lilo?
LILO: Ana cewa 'Lilo Lilo dan mazarina!' Domin duk abin da aka kira mazari, to ana nufin rawa kenan. To saboda rawar ne mutane ke cewa Lilo, shi ne sunan ya tashi a haka.
Saboda ganin ka shekara a wajen rawa to akwai wasu wadanda ka koya mawa har su ma suka shahara?
LILO: E rawa kam, ai an ce ba don makoyi ba da gwani ya kare. Ita harkar rawa, kana iya koya wa mutum rawa, a gobe ya fi ka iyawa. Saboda haka ita rawa ba a yi mata fariya kuma ba ta da gwani. Yauwa. Ni rawar nan tsintar kaina na yi a ciki kuma ina da magabata da suka koya min. Ka gane? Bayan haka akwai wadanda na koyar wadanda ba za su kirgu ba a nan Jihar Kano da wajen Kano, e ba su da adadi. Don na koya wa kungiyoyi da dama saboda in kai ne yau, gobe ba kai ba ne.
Ku ne kuka sa rawa ta karbu a harkar fim. To ban da rawa kana taka wani matsayin a fim?
LILO: A gaskiya ko a da can, tun kafin fim, mukan yi diramar dabe. Muna da wata kungiya tamu ta musamman a unguwar Tarauni, wadda yake kungiyar nan tana daya daga cikin wadanda suka fara diramar dandamali a Kano. Da ma can na yi dirama kafin a fara wasa. Irin wadannan raye-raye kuma a lokacin babu wata kungiya da take kada ganga ta yi rawa in ba Hukumar Tarihi da Al'adu ba-kafin ma in fara aiki da su kenan. Daga wannnan rawar koroso da ake yi sai na ga ya dace mu ma kungiyarmu ta shigo da irinta.
Can baya ka ce rawa ba ta da gwani, amma ai kai idan kana yi za mu ga kana lauya gabobin jikinka kamar wani ibilishi.
LILO: Ai ka san an ce yabon kai jahilci. Ni dai a harkar rawa ban dauki kaina komai ba. Sai dai kawai ina iyakar bakin kokarina in taka ta daidai iya sanina. In akwai wadanda za su zo su taka rawar nan ya kasance sun fi ni ko kuma jama'a sun fi sha'awar abin da suka yi a kan wanda na yi. Ni har gobe ban dauka cewa na iya rawa ba.
Daga lokacin da ka fara lankwasa jikinka kana rawa, akwai sa'ada ka taba gocewa ko gurde kafa?
LILO: In kana jin gurdewa ai daya kenan. Ni ba zan taba mantawa ba, akwai lokacin da muka je Kaduna za mu taya 'yan makarantar Kaduna Polytechnic wata murna. Da muka hau sama bai fi saura minti biyar a fara wasa ba, garin gwada wani dan juyi sai na fadi. A nan na fara fitar da jini ta goshi. A daidai lokacin kuma aka kira mu za mu yi wannan rawa. Sai na ajiye ciwo waje daya, na shiga na gama wannan rawar, na dawo ina jinya. Sai gurdewa ta gwiwa. Akwai lokacin da muke wasa a 'Yar Gaya, nan ma da yake ba wasan dabe ba ne, ni ne nake jan rawar. Ina kallon na bayana, sai na jefa kafata cikin wani rami. Nan kafata ta gurde, sai dai dauke ni aka yi. To irin wadannan akwai su da yawa.
Kamar yadda ake ganin kuna tsalle kuna wakitawa tare, shin kuna yin gwaji kafin ku fara ne ko kuwa?
LILO: Muna wahala wurin gwaji sosai, saboda idan ka zo ka ga yadda muke wahala wurin gwajin wannan rawar ko tsalle-tsallen kamar yadda ka ce, sai ka tausaya mana. Wani lokaci ma da bacin rai za mu rabu saboda kowa na neman daidai. Amma da yake yau da gobe ta fi karfin wasa, mun riga mun saba. Shi ya sa mu idan muna yin ba mu tausayin kanmu, sai dai wanda ke kallonmu shi ke tausaya mana.
Ka ce ka koya wa mutane da yawa. Hausawa kuma na cewa babu malamin da ba shi da malam; to kai waye malaminka?
LILO: A gaskiya malamaina suna da yawa. Da farko dai zan kira maka wadanda ke gabana sai dai da yake mun taso mun zo daidai muke tafiya a haka. Na farko kamar su Muntari Kwanzuma, John Flash, su Lilisco, su Muntari Kwamared da sauransu. Duk wadannan a gaba suke da ni a rawa. To amma ka san yadda muka zama daya muna taimakon kanmu da kanmu.
Wane jarumin fim ka fi jin dadin rawa da shi?
LILO: A gaskiya akwai mutanen da muke jin dadin rawa tare da su. Duk mutumin da aka ce jarumi ne ko jaruma yawancinsu muna jin dadin harkar da su idan mun zauna mun shirya yadda za a yi rawar. Kuma ka san akwai wadanda su ba rawa suke yi ba idan suna bin waka, kamar su Musbahu M. Ahmad, amma a bangaren masu rawa akwai irin su Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu, Idris Shu'aibu Lilisco, Sani Musa Mai Iska, da sauransu. A mata ka ga kamar Fati, su Biba, sukan yi kokari.
Na san mutum ya niko gari kuma ya bare a cikin rairayi ai ba zai ji dadi ba, to ya ka ji lokacin da aka ce an hana rawa? Kuma ka san fa har yanzu akwai masu sukar rawa a fim.
LILO: Ai na ji damuwa kwarai da rashin jin dadi da bakin ciki. Saboda rashin sanin muhimmancin rawar ne a fim ya sa (mutane) suke fadar wadannan maganganu a baya, bayan sun ga fim din ya karbu. Saboda ba mu da abin kallo a da face finafinan Indiya da sauransu. Ta ya za mu jawo hankalin mutanenmu daga raye-raye ne da wake-wake da muke yi su ne yake kara jan hankalin mutanenmu suke dawowa suna kallon finafinan Hausa.
Yanzu gani suka yi fim din Hausa ya karbu ana sha'awarshi ko'ina ya sa suka turo wannan maganar. Ai ba wani abu ba ne, idan an kawo wannan maganar, ai rawa al'ada ce; idan ba ka yi ba ubanka ya yi, idan ubanka bai yi ba, kakanka ya yi; in kakanka bai yi ba, 'yan'uwanka sun yi. A biyo asali a gani. Ba mu da rawa a gargajiyance? Saboda haka, ba wai mun ki abin da suka fada ba, yadda za a bullowa wa wannan lamari shi ne, idan mutum ya ce shi bai da ra'ayin kallo, to kada ya gani. Amma idan an raba masu so, kashi 90 suna so. To don kashi 10 ba su so sai me? Dole raina ya baci saboda na san wadanda ke cin abinci ta hanyar raye-raye da wake-wake, ba za ka iya lissafa su ba.
Ko don gudun irin haka ne ya sa mukan ga kakan dan fito a cikin finafinai shi ya sa kake kokarin jirkicewa?
LILO: Da ma ni jirkitacce ce! Tun farko ni dan dirama ne. Babu irin wasan da ban yi-daga na mai kudi, na talaka, na barawo, na dan iska, kai ni kowane wasa aka ce in yi zan yi.
To ka yanke shawarar lokacin da za ka daina rawa, ko sai tsufa ya kama ka ka fara dogara sanda?
LILO: Wannnan kam ba ta taso ba. Don ita rawa tana da lokaci. Akwai lokacin da ko an ce ka yi rawa, ba za ka yi ba. Shi ne dalilin da ya sa muke koya wa na kasa.
Matanka nawa kuma 'ya'yanka nawa?
LILO: Ni yanzu yadda ake bin tsarin a yi aure ma ban sani ba. Abin da na sani dai shi ne a gayyace ni daurin aure, in je a shafa Fatiha a yi harkokin biki. Saboda haka ban da aure, haka nake zikau. Sai dai nan gaba in Allah ya yarda zan yi.
Ba ka da aure amma ga shi har wasu na yi maka kallon ka tsufa don suna ganinka da sanko?
LILO: Sankon rawa ne ba na tsufa ba ne, ai sankon rawa ne wannan (dariya har da kyalkyatawa). Sankon rawa ne da kudi-amma yanzu rawar ce ta fara zuwa, kudin kuma suna nan tafe, sauran kadan sun kusa zuwa.
Ko kun taba yin wata bajinta ta dalilin rawa?
LILO: Abin da zan fara fada shi ne mun yi wa Jihar Kano bajinta saboda a bikin al'adu na gasar NAFEST mun dauko kofi mun kawo Kano har sau uku. Mu ne muke zuwa na daya, mu kinkimo kofi mu kawo Jihar Kano.
Sai kuma bajinta ta kasashen waje da na je: Amerika, Chaina, Faransa, Iran, Benezuela, da sauransu. A nan Afrika kuwa duk kasashen da muka je, muna kara fito da sunan Kano saboda idan mun yi rawa, mutane suna sha'awa, suna rungume mu suna yaba mana.
Idan za ku tafi da gangunan kida kuke tafiya ko kade-kade kuke dauka a cikin kaset na rikoda?
LILO: Ai idan za a yi irin wannan tafiya ana tafiya da komai da komai ne, ba wai a dauki kida a kaset ba. A'a, da ganguna ake tafiya.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin