Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 35   Nuwamba 2002
TALLA


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
TALLA
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Duniyar Finafinai
Rahoto
Malam Zurke
Rayuwarmu
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Wa zai fi cancantar zama Gwamna?

Kaduna sai Mairago!
Alh. Yusuf Hamisu Abubakar (Mairago)

A MATSAYINSA na tsohuwar hedikwatar Jihar Arewa, Kaduna gari ne na wane da wane, musamman gaggan 'yan siyasa, masu hannu da shuni, da kuma manyan sojojin da suka yi ritaya. Amma abin mamaki game da siyasar Kaduna, mafi yawancin manyan 'yan siyasar da ke zaune a cikinta sun fi maida hankali ga siyasar da ta shafi jihohinsu na haihuwa. Misali, Alhaji Umaru Shinkafi ya fi bada karfi ga siyasar tsohuwar Jihar Sokoto fiye da ta Kaduna. Haka su ma Adamu Ciroma a jihar Yobe, Lema Jibrilu, Lawal Kaita, Musa Musawa, Wada Nas, da kuma Janar Buhari mai ritaya, duk sun fi damuwa da siyasar jiharsu fiye da ta wata jihar.

To in haka ne, yanzu su wanene masu fada a siyasar Jihar Kaduna? Mecece makaomar siyasar jihar? Shin Gwamna Ahmed Mohammed Makarfi zai iya ci gaba da rike wa jam'iyyar PDP kujerar da yake a kai yanzu? Ya ake ciki game da koke-koken mika mulkin Jihar Kaduna ga 'yan Kudancin jihar ?

Wace dama matasan 'yan takarar kujerar gwamnan jihar irin su tsohon shugaban karamar hukumar Giwa, Alh. Lawal Abdullahi, da kuma mutumin kirki da saukin kan nan Alh. Yusuf Hamisu Abubakar wanda aka fi sani da Mairago za su samu?

Duk da irin rawar da take takawa, ba ma a Arewa kadai ba har a kasa baki daya, Kaduna tana da karancin gaggan 'yan siyasa, wato mai iya tsare gida ya ce lallai sai wane zai hau kujerar gwamna, kamar yadda Sola Saraki yake yi a Jihar Kwara. Mutane irin su Umaru Dikko da Balarabe Musa za a iya cewa ko dai ba su shirya ba, ko kuma yanayin siyasar bai yi masu ba. Ba kamar Jihar Katsina ba, inda gwamnanta yake cin albarkacin dan'uwansa marigayi Janar 'Yar'Aduwa, ko kuma Kano inda Kwankwaso ya samu daurin gindi daga suAbubakar Rimi. Ba kuma kamar Sokoto ba inda ake siyasar rikau, ko Kano inda ake siyasar tsageranci, siyasar Jihar Kaduna ba ta tsageranci ba ce kuma ba ta rikau ba ce; ta sha bamban da ta sauran jihohi shida da ke yankin Arewa-maso- yamma na kasar nan, saboda a nan ne kawai ake amfani da addini da kabilanci wajen neman kuri'u.

Shekaru uku da suka wuce, Alh. Ahmed Mohammed Makarfi ya zama Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin tutar jam'iyyar PDP bayan ya kayar da abokin takararsa, Alh. Suleiman Zuntu na jam'iyyar APP a da. Makarfi ya samu goyon bayan matasan 'yan siyasa ta fuskar hangen za a samu ci-gaba mai dorewa.

Bayan shekaru uku sai labari ya canza, yanzu ya zamanto ana zarginsa da abubuwa da dama. Da yawa daga cikin masu son tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar a cikin shekarar 2003, tuni sun wasa wukakensu. To amma a ina ne Makarfi ya gaza? Kuma menene natsalolinsa? Akwai masu zarginsa da rashin iya gudanar da mulki yadda ya kamata, wanda a cewarsu shi ya jawo rikicin addini da aka yi a Kaduna a cikin 2000. Da yawa na ganin in da a ce ya dauki matakan da suka kamata a lokacin, to da rikicin bai faru ba. Sun ce a lokacin ya tafi neman magani a kasar waje wanda hakan ya nuna rashin cancantarsa, kamar yadda Zuntu yake cewa a wata muhawarar takarar kujerar gwamna. Shi ma tsohon mataimakin gwamnan jihar, Mr. James Bawa Magaji, haka ya ce kwanan baya. Ita ma Masarautar Zazzau ana hangen ba ta ji dadin yadda Makarfi ya kacaccala ta ba tare da rage mata karfi. Masu lura da al'amuran siyasa a jihar suna ganin masarautar ba za ta ba gwamnan goyon baya ba. Hatta mazauna kudancin jihar suna ganin farin jinin gwamnan ya rage idan aka yi la'akari da abin da ya faru a Kafanchan lokacin da mataimakin shugaban kasa ya kai ziyara can. Duk da cewa Makarfi ya kirkiro masu sababbin masarautu, inda a ganinsu ya kubutar da su daga 'mulkin danniya' na Hausa-Fulani a yankin, har ila yau suna jin haushin ya ki nada shugabannin da jama'a ke so, amma ya nada nasa.

An samu labarin cewa Makarfi yana da hannu wajen korar da gwamnatin tarayya ta yi wa Alh. Sulaiman Zuntu daga mukaminsa na shugaban Hukumar Fadamun Kogin Neja. An kuma zarge shi da rubuta wa shugaban kasa wasika yana son a tsige Yusuf Hamisu (Mairago) daga mukaminsa na babban sakatare na Hukumar Asusun Inganta Fasahar Ma'adinan Man Fetur (PTDF) ta kasa.

Daga yankin da gwamnan ya fito kuwa, tuni wani matashi kuma tsohon shugaban karamar hukumar Giwa, Alh. Lawal Sama'ila Abdullahi, shi ma ya fito neman tsayawa takarar gwamnan jihar. Ana kuma zargin Makarfi da cewa ya taba neman a cire Alh. Rilwanu Lukman daga mukaminsa na shugaban Kungiyar Kasashe Masu Albarkatun Fetur ta Duniya (OPEC) a cike gurbin da wani dan Jihar Kaduna saboda wai yana mu'amala da Furofesa Ango Abdullahi, wanda ba ya goyon bayan shi Makarfin ta fannin siyasa.

Shi kuwa Sanata Musa Bello, ana sa ran zai mara wa Mairago baya ne musamman saboda Makarfi ya ce bai yi da shi saboda wasu kudi da gwamnatin jihar take binsa na wata kwangila da aka ba shi a zamanin Dabo Lere wadda bai yi ba.

Haka kuma lokaci kadan da ya wuce Makarfi ya yi hannun-riga da kwamishinan kudi na jihar, Alh. Suleiman Hunkuyi, wanda kuma a da shi ne sarkin yakin kamfen na Makarfin.

Kuma ana zargin mukarraban Makarfi da laifin tsoratar da magoya bayan Mairago, musamman zancen kama wasu matasa da aka yi saboda suna ta manna hotunansa a cikin garin Kaduna.

Game da hanyoyi da samar da lantarki kuwa, an yaba wa Makarfi, amma abin da mutane ke tambaya shi ne, nawa aka kashe wajen aiwatar da ayyukan, kuma su wanene suka amfana da kwangilolin? A yanzu haka gwamnan yana shari'a da Janar Joshua Madaki a kan bai wa wani kamfani mai suna Syntax inda aka ce na su Makarfi ne kwangila da kuma wasu zarge-zargen da ake yi masa a kan mallakar filaye a sassa daban-daban na jihar. Ganin yadda yakin neman zabe ya yi zafi a Jihar Kaduna mutane sun zaku su ga wanda zai iya hawa kujerar gwamna a jihar in har Makarfi ya kasa cin zabe a karkashin jam'iyyar PDP. Da yawa sun tsorata, suna ganin maganar ta-zarcen Makarfi kamar mafarki a saboda fitowar sanannen dan takara irin Alh. Yusuf Hamisu Abubakar duk da cewa bai fito fili ya bayyana ra'ayinsa ba. Akwai yiwuwar yin hakan idan aka yi la'akari da abin da dakarun yakin zabensa suka gaya wa shugaban PDP na jihar kwanan nan.

Makarfi zai sha mamaki duk da kasancewarsa yana kan mulki, saboda ba karamin shiri Mairago ya yi ba. Manyan mutane daga fadar shugaban kasa, wadanda Makarfi ya kuntata wa, a shirye suke su ga sun kada shi. Idan har ya samu cin nasarar haye zaben share fage saboda kasancewar mulki na hannunsa, to wata jam'iyyar za ta iya lashe zaben zama gwamnan jihar musamman idan Mairago, Lawal da Hunkuyi suka yi masa taron dangi suka goyi bayan abokin hamayyarsa.

An fassaro daga jaridar Weekly Trust ta ran 25 ga Oktoba, 2002

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin